Ingantattun sunaye na musulunci article
Barka yan'uwa da wannan lokaci kuma barkanku da zuwa wannan shafi namu mai ɗauke da sakon ilimi iri daban-daban. A yau idan Allah ya nufa zamu yi magana ne akan sunaye masu ma'ana da inganci wanda muka sawa ingantattun sunaye na musulunci kuma zamu yi duba mai zurfi domin samar da wayewar kai sosai.
Menene suna
Kafin mu wuce izuwa gaba yana da kyau musan menene suna a cikin wannan rubutu na ingantattun sunaye na musulunci, suna yana nufin duk wani laƙabi da ake amfani dashi wajen kiran mutum wanda shima kansa ya yarda cewa eh wannan sunansa ba tareda wani kokwanto ba. A wata ma'anar zamu iya bayar da cewa suna wata inkiya ce ta kalma wadda take amfanuwa wajen yin kira da nuni akan abinda ake nufi.Idan aka ɗauki suna musamman sunayen mutane tunda a kansa muke magana zamu ga cewa babu wani mutum a wannan duniya wanda ya raɗawa kansa suna, kowa kawai ya tashi a rayuwarsa yaji ana kiransa da wani laƙabi wanda idan bada wannan laƙabi ka kirashi bama to fa bazai amsa maka ba.
A wannan rubutu namu na ingantattun sunaye na musulunci ko muce sunayen da shari'a ta aminta dasu zamu iya raba suna izuwa iri guda biyu.
1. Sunayen banza
2. Sunayen kirki
Sunayen banza
Cikin sauƙi kamar ya nuna sune duk waɗansu sunaye wanda shari'ar Islama bata amince dasu ba wato su basa cikin ingantattun sunaye na musulunci misalin irin wadannan sunaye sune kamar haka.
1. Tamangi
2. Jizga
3. Kiyo
4. Fan-beguwa
5. Gwarbai
Kamar yadda sunayen dake sama suka nuna irin wannan sunaye basu da wata ingantacciyar ma'ana a cikin addinin Musulunci. Ko ba'a faɗa ba irin wannan sunaye basa da wani amfani a dinga amfani dasu a rayuwar yau da kullum.
Sunayen kirki
Sunaye masu kyau da magana kenan wanda kuma amfani dasu shine dai dai a wannan rayuwa. Sunayen kirki sune duk wasu sunaye da zamu iya amfani dasu ba tareda jin wani nauyi a zuciyarmu ko rashin jindadi, kuma zamu iya yi musu laƙabi da ingantattun sunaye na musulunci domin kuwa addini ya aminta dasu yadda ya kamata. Kai da kanka koda ba'a faɗa maka zake gane cewa sunane masu ma'ana da tushe. Sunayen annabawa, manzanni, da sunayen mutanen kirki duka zasu iya shiga cikin wannan fanni kai harma da sunayen mu na gargajiya. Misalin irin wannan sunaye sune kamar haka.
1. Muhammad
2. Iliyasu
3. Musa
4. Ɗan ladi
5. Tanko
Duk sunan dake da ma'ana mai kyau tofa sunan kirki ne kuma zai iya shiga cikin ingantattun sunaye na musulunci wato kaga kenan da yawa daga cikin sunayen al'ada zasu iya shiga wannan bangare.
Jerin ingantattun sunaye na musulunci na mata:
Na addini:
1. Fatima
Sunane mai matuƙar tushe da asali domin kuwa sunan diyar annabi Muhammad ce kuma yar lelensa. Wannan suna yana ɗaya daga cikin ingantattun sunaye na musulunci kuma wanda zamu iya cewa na gaban goshi.
2. Aisha
Shima wannan suna sunan manya ne domin kuwa sunan matar Annabi ce mai daraja.
3. Maryam
Sunan mahaifiyar Annabi isah sunan mace ne mai ƙima da daraja kuma shima yana daga wannan suna na ingantattun sunaye na musulunci na mata.
4. Khadija
Sunan matar Annabi ta farko ce kuma mai girma da daraja wacce take da matuƙar ƙoƙari akan harkokin musulunci.
5. Mariya
Itama sunan matar Annabi ne kuma masoyiyarsa suna ne na mutuniyar kirki mai girma na ingantattun sunaye na musulunci.
6. Amina
Mai girma mahaifiya ga mai girma asalin sunan mahaifiyar Annabi ce wadda muke girmamawa a kullum da ko yaushe. Yana kyau ka sawa yar ka wannan suna.
7. Zainab
Yana ɗaya daga cikin ya'yan Annabi Muhammadu suna ne mai kyau da asali.
8. Rukayya
Shima yana ɗaya daga cikin ingantattun sunaye na musulunci wanda sunan diyar annabi ce.
9. Habibah
Ma'anarsa shine masoyiya ta masoyi wanda shima sunane mai kyau kuma na mutanen kirki.
10. Jamila
Mai kyau shine ma'anar wannan suna kuma yana daga cikin ingantattun sunaye na musulunci na matan hausawa ko larabawa.
Na gargajiya:
1. Dela
Dela itace matar da aka haifa bayan haihuwar maza, wato yayyanta du maza ne. Irin wannan suna yanzu zaiyi wuya kaji ana amfani dashi a birane kuma sunane mai kyau domin addini bai hana amfani dashi ba shiyasa muka sako shi a cikin ingantattun sunaye na musulunci.
2. Gambo
Macen wacce ta biyu bayan tagwaye a haihuwa ita ake kira da gambo. Shima sunane mai na gargajiya.
3. Yar auta
Wannan ko ba'a faɗa ba za'a gane cewa itace wacce aka haifa a ƙarshe a gida wato yar lelen mama kenan. shima yana daga cikin ingantattun sunaye na musulunci.
4. Sadau
Duk yarinyar da aka haifa bayan iyaye sun rabu wato Bayan anyi saki ita muke cewa Sadau, shima ana iya amfani dashi wajen sunan jaririya wacce irin hakan akan iyayenta.
5. Cindo
Ƙarin halitta na yatsa shi muke cewa cindo a hausance shima ba suna ne mara kyau ba domin har izuwa yanzu iyayenmu na amfani dashi. koma nace mai iya saka shi a ingantattun sunaye na musulunci.
6. Kyauta - Rabo
Bayan wani gajeren bincike da muka gudanar munyi nasarar sami ma'anar wannan suna na Rabo ko Kyauta wanda yake nufin yaro ko yarinyar da aka haife ta bayan dogon lokaci ba'a samu haihuwa ba.
7. Ajuji
Yarinyar da ake kira da ajuji itace wadda aka haifa bayan samun rashe rashe na yan uwanta wato sai a kanta ne Allah ya raya.
8. Wada
Shima yana daga cikin ingantattun sunaye na musulunci wanda ke nufin wacce aka samu albarkar kayan barka bayan aihuwarta.
Jerin ingantattun sunaye na musulunci na maza:
Na addini:1. Muhammad
Na farko a komai da komai sunan fiyayyen halitta annabi mai girma, shima ko kokwanto babu yana daga cikin ingantattun sunaye na musulunci wanda maza ka iya amfani cikin girmamawa.
2. Musa
Sunan ɗaya daga cikin manya-manyan annabawan Allah mai rahama mai jin kai, wanda ya samu yardar Allah tayin zance dashi. shima suna ne ingantacce.
3. Ayuba
Suna ne na annabin Allah mai girma shima yana daga cikin ingantattun sunaye na musulunci.
4. Abdullahi
Ma'anarsa shine bawan Allah sunan mutanen kirki ne masu girma.
5. Aminu
Amintacce abun aminta suna ne mai kyau da asali domin kuwa sunan Annabi ne. shima zamu saka shi daga gaba gaba a cikin ingantattun sunaye na musulunci.
6. Suleman
Mai mulki da girma wato shiɗin Annabi ne maɗaukaki kuma wanda ya samu girmamawa daga Ubangijinsa.
7. Dawud
Sunan mahaifin annabi suleman ne kuma Annabi mai girma daga annabawan Allah mai girma. zai shiga cikin wannan jeri na ingantattun sunaye na musulunci.
8. Yusif
Sunan Annabi kuma ɗan gidan Annabi, kyakkyawa daga Allah, sunane mai asali da daraja.
9. Aliyu
Sahabin Annabi ne kuma ɗan uwansa wanda ya bayar da gudummawa mara misaltuwa domin cigaban yaɗuwar addinin Allah a ban ƙasa. shina a iya amfani dashi akan jarirai masa domin yana daga cikin jerin ingantattun sunaye na musulunci.
10. Hamza
Zakin Allah, sahabin Annabi kuma mai girma da ɗaukaka.
Na gargajiya:
1. Rabo
Ma'ana shine yaron da aka same shi bayan lokaci mai tsayi ana neman aihuwa.
2. Gambo
Wanda aka haifa bayan haihuwar tagwaye.
3. Auta
Na karshe a haihuwa yana daga cikin ingantattun sunaye na musulunci masu ma'ana na gargajiya.
4. Ɗan Ladi
Sunan gargajiya ne wanda ke nufin mutumin da aka haifa ranar Lahadi.
5. Ɗan Liti
Shima wannan suna ne mai kyau domin addini ya aminta dashi, ma'anarsa shine wanda aka haifa ranar Litinin.
6. Mai Nasara
Nasara abu ne mai kyau shiyasa ma ya shiga jerin ingantattun sunaye na musulunci.
7. Gwani
Ƙwararre a fannin aiwatar da wani abu ko wani aiki shi muke cewa gwani, sunane wanda har ana amfani dashi a wasu wuraren.
8. Malam
Iyaye sukan iya sakawa dansu suna malam musamman idan yanada sunan mahaifin maigida. sai ayi masa laƙabi da malam domin nuna girmamawa ga sunan. shima yana jerin ingantattun sunaye na musulunci na maza.
9. Ɗan azumi
Mutum mai yawan azumi akan iya laƙabaasa wannan sunan ko yaron da ake masa fatan ya kasance mai yawaita yin azumi.
10. Sallau
Shima wannan suna ne mai kyau da asali kuma nuni da mai yawan sallah.