Maganin farin jinin sama

Maganin farin jinin samari

A rayuwa ta yau da kullum ubangiji Allah bai hana mana neman magani akan komai ba illa iyaka dai ya hana bin hanyoyi marasa kyau domin neman magani akan wata matsala taka rayuwa. A koda yaushe abu mai kyau shi yafi inganci da amfani akan mara kyau, ki kasance mai bin mai kyau mai inganci domin girmama kanki da ahalinki. Linzamin alƙalamin yau yayi juyi izuwa rubutun maganin farin jinin samari gamida jawabin maganin farinjini na musulunci bamu tsaya nan ba akwai addu'ar farinjini, wuridin farinjini dama lakanin dama wasu abubuwa masu alaƙa da hakan.

Maganin farin jinin samari

Menene farin jinin samari:

Farin jinin samari abu ne mai matukar amfani da dama a wajen yan mata domin samun kulawa daga wuraren samari masu yawa, duk da wasu suna ganin kamar ba abu ne mai kyau ba idan budurwa tana da yawan samari, amma har yanzu abinda ba'a gane ba shine duk mace mai farin jinin samari tofa gaskiya tana tara samari da yawa masu son ta. 

Wannan farin jini shike sa wasu yan'matan su zamto masu girman kai wasu kuwa su kanyi amfani da baiwa ta ubangiji domin ginawa kansu rayuwa mai kyau wato su sami namiji guda wanda ya amsa sunansa namiji suyi aure su rufawa kansu asiri. 

Ana iya samun maganin farin jinin samari daga wasu hanyoyi amma kuma wasu basa amfani da wani maganin farin jinin samari kawai a haka Allah ya halicce su, wato zaka gansu Allah ya hore musu farin jini daga samari.

Akwai ire iren Maganin farin jinin samari wanda addini ya aminta dadu akwai kuma maganin farin jinin samari wanda addinin Islama bai amince dashi ba. 

Maganin farin jinin samari wanda addini bai yadda dashi ba:

Irin wannan magunguna kwata kwata addini bai yarda dasu ba shine dalilin daya saka muma ba zamu yi bayani akansu ba, misali zuwa wajen malaman tsiɓɓu da bin bokaye domin neman magajin farin jinin samari. Wannan kwata kwata bashi da kyau ayi hattara domin kuwa zaki iya janyo wa kanki fushin ubangiji maɗaukaki.

Maganin farin jinin samari a musulunci:

A wannan ɓangare munzo dai dai inda ya kamata muyi iya bakin ƙoƙarinmu domin kawo muku ingantattun bayanai masu amfani domin samun dacewa akan abinda kuke buƙata yan'mata. Maganin farin jini domin jan hankalin saurayi ko samari sunanan daban kala kala. kamar irinsu;

1. Addu'ar farin jini a musulunci

Akwai addu'o'i da yawan gaske wanda ake yinsu domin neman yardar Allah akan farin jinin samari: A duk lokacin da zaki a fita daga gida domin zuwa aike ko zuwa zumunci, saiki tsaya a tsakiyar gidanku sai ki karanta (Alam-nasharaha) kafa tara 9 sannan ki tofa a hannun damanki saiki shafe fuska sannan ki dsga fita kullum idan zaki ko lokacin da kika samu damar fita sai kiyi hakan. Da iznin Allah duk wanda kuka yi arangama dashi a hanyarki tofa sai yaji kinyi masa sai dai kuma yanayin halin namiji wani bazai nuna miki kinyi masa ba, sai ki dage domin yin hakan.

2. Wuridin farin jini

Akwai wuridai suma da ake yi domin farin jinin samari kamar haka:

Bayan kinyi sallar insha'i kullum ki zauna kada ki tashi daga inda kike ki dinga - Ya Rahmanu -Ya Rahmanu sai kinyi kamar ƙafa dari biyu da hamsin ko sama da haka kada kai ya gaza haka, sannan sai ki rufe da (ƙul-wuhallahu) kafa bakwai ki shafe fuska.

3. Lakanin farin jini

Laƙanin farin jini da tumfafiya

_ Ki yawaita cin furen Tumfafiya domin yana matuƙar janyo hankalin samari ko yasa ki zamo mai farin jini.

_ Garin furen Tumfafiya ana amfani dashi wajen zubawa a cikin ruwa a dinga wanke fuska dashi duk lokacin daya samu.

_ Zuba garin furen Tumfafiya a cikin abinci yayin ci yana sanya ki zamo mai farin jini sosai. 

_ Sanya furen Tumfafiya a cikin jakarki yayin zuwa unguwa yana sanya wa ki zamo mai kwarjini da farin jini bama ga samari kaɗai ba harma da sauran jama'a.

_ Ana haɗa furen Tumfafiya gamida furen bishiyar zaitun duk a zuba su a gauraya a cikin man shafawa a rinƙa shafawa a jiki shima wannan yana matuƙar kawo farin jinin samari.

_ Idan aka sanya icen Tumfafiya a gida to shima tabbas yana kawo farin jini da izinin Allah. Duk da wasu suna tunanin Tumfafiya na ɗauke da aljanu wannan du ƙarya ne kawai. Itaciya ce kamar sauran itace.

4. Farin jini daga Allah

Mace mai rin wannan farin jini na halitta bata da buƙatar dole sai tayi wani shafe shafe domin ita Allah ya hutar da ita sai dai kuma yan magana sun ce idan kanada kyau ka ƙara da wanka. Wannan baiwar Allah ce ya bawa wanda yaso sannan ya hana wanda yaso.

Anan muka kawo karshen wannan rubutu namu mai suna maganin farin jinin samari.

Post a Comment

Previous Post Next Post