Sunayen mata da ma'anarsu

Sunayen mata da ma'anarsu

Barka da zuwa wannan gida mai albarka, a yau idan Allah ubangiji mai duka ya nufa, alƙalamina zai karkata izuwa bayanin yadda sunayen mata da ma'anarsu yake a arewacin Najeriya ko kuma nace sunayen mata da ma'anarsu a al'ummar hausawa.

Sunayen mata da ma'anarsu

Hausawa a shekarun baya sun kasance masu matuƙar amfahari da sakawa yayansu sunayen gargajiya, amma yanzu a wannan zamani kowane saurayi yayi aure to yawanci gaskiya anfi amfani da sunaye masu daɗi wanda suke kama dana yan gayu. Amma hakan baya nufin cewa an watsar da sunayen gargajiya domin kuwa har izuwa yanzu da nake maka wannan rubutu to akwai wuraren da suke amfani da sunayen gargajiya.

Saidai kuma idan zaka ƙiyasta yawan adadin jarirai da ake sakawa sunayen gargajiya a yanzu yayi ƙasa sosai. Domin kuwa baya wuce kashi goma cikin ɗari na yaran da ake haifa 10/100.

Misalan wasu daga cikin sunayen mata da maza da ma'anarsu na gargajiya:

1. Dela

2. Tanko

3. Audi

4. Jakin tagwaye

5. Gambo

6. Auta

7. Sadau

8. Cindo

9. Kyauta - Rabo

10. Ajuji

11. Wada

12. Shekarau

Fassarar sunayen mata da ma'anarsu na sama:.

1. Dela

Idan kaji ana cewa mace Dela a cikin al'ummar hausawa, to itace macen data biyo maza. Abinda ake nufi data biyo maza shine, bayan mahaifiya ta haifi ya'yanta sai ya kasance yawancinsu duk ya'ya maza ne, misali kamar ace bayan haihuwar yara maza huɗu ko kuma sai ta shidan ta kasance mace. To a gargajiyance ana kiranta da suna Dela.

2. Gambo

A cikin wannan rubutu namu na sunayen mata da ma'anarsu, mun sako sunan Gambo ne a wannan ɓangare domin zai iya kasancewa sunan mace ce ko kuma namiji, wato kowane ɓangare suna amfani da wannan suna. Amma kai tsaye mace mai suna Gambo itace wadda ta biyo yan biyu wanda muke cewa tagwaye.

3. Yar auta 

Yar auta Itace macen data kasance a ƙarshen haihuwa, yan gatan iyaye musamman ma uwa, domin hausawa suna matuƙar ji da yan auta, komai suna iya samu daga wajen Iyaye ba tareda wata tangarɗa ba.

4. Sadau 

Ma'anar sunan Sadau shine yarinyar da aka haifa bayan rabuwar iyayenta, wato Allah ya kawo rabuwar aure tsakanin mahaifanta kuma bayan anyi rabuwar Allah ya kawo rabon samunta. To a cikin sunayen mata da ma'anarsu wannan ita ake cewa Sadau. Amma bawai iya mata kaɗai ke ɗaukar sunan ba, ta ɓangaren maza ma ana samu.

5. Cindo 

Duk jaririyar da aka haifa da ƙaruwar yatsa a hannu ko kuma a ƙafarta ita ake cewa Cindo, wato mai ƙarin abun halitta.

6. Kyauta - Rabo 

Bayan ɗan ƙaramin bincike a rubutun sunayen mata da ma'anarsu, munyi nasarar samun ma'anar sunan rabo ko kuma ace kyauta, wato itace yarinyar da aka haifa bayan shafe lokaci ko shekaru masu tsayi ba tareda samun haihuwa a wajen mahaifanta, kasan ko ba'a faɗa ba zata kasance yar gata ta gaban kwatance.

7. Ajuji

Macen da ake kira ajuji itace wacce aka jarirai da dama amma Allah bai raya ba sai a kanta, wato yarinya yar sa'ar iyaye. Kai wasu ajujin har sai an cire rai akan cewa zasu rayu sai kuma Allah ya raya.

8. Wada

Wada ko kuma muce yar wada, Itace macen da aka samu albarkar kayan barka bayan aihuwarta, wato yan'uwa da abokan arziki sunyi gudunmawa yadda ya kamata domin nuna farincikinsu da samuwarta.

Sunayen wasu daga cikin sunayen da ma'anarsu:

1. Tanko

Namijin daya biyo mata a haihuwa wato wanda aka haifa bayan kamar mata biyu ko uku ko sama da haka.

2. Audi

Shine wanda tun yana ciki mahaifinsa ya rasu, kaga kenan shine wanda aka haifa ba tareda da ubansa yana raye ba.

3. Jakin tagwaye

Shi kuma wannan shine wanda yan biyu ko tagwaye suka biyo shi wato saida aka haifeshi sannan aka samu tagwaye.

4. Gambo

Wanda ya biyo yan biyu a haihuwa.

5. Auta 

Namijin daya kasance na ƙarshen haihuwa a wajen iyayensa.

6. Sadau

Yaron daya zo duniya bayan iyayensa sun rabu, wato bayan anyi rabuwar aure wadda muka fi sani da saki sai kuma aka haifeshi.

7. Cindo

Duk jaririn da aka sameshi da ƙarin yatsa a ƙafarsa ko a hannayensa.

8. Kyauta - Rabo

Namijin da aka haifa bayan bayan lokaci ba haihuwa.

9. Ajuji

Yaro ɗan sa'a kenan wato yarone wanda saida aka sha gwagwarmaya sannan aka samu ya rayu, duk yan'uwansa sun rasu sai a kansa Allah ya raya.

10. Wada

Wanda bayan haihuwarsa an samu kayan barka da yawa.

11. Shekarau

Wanda ya shafe tsawon lokaci a cikin Mahaifiyarsa kafin a haifeshi.

Sunayen mata da ma'anarsu a zamanan-ce:.

Waɗannan sune sunayen da hausawa ke sakawa yayansu wanda ake yi musu laƙabi dana yan gayu wato na yan zamani. Kuma abin mamakin-ma shine yawancinsu du sunayen larabawa ne. Kaga kenan musulunci ce wanda annabin-mu ya yadda dashi. Amma hakan baya nufin sunayen gargajiyarmu addini bai yadda dasu ba. 

1. Iman

Ma'anar sunan Imani shine imani da hausa, wato yadda da miƙa wuya da kasantuwar ubangiji maɗaukakin sarki mai kowa mai komai ( I love you Allah ). Wannan suna yanada kyau sosai, zaka iya amfani dashi akan yarka.

2. Amira 

Yana nufin gimbiya shima sunane mai kyau a jerin sunayen mata da ma'anarsu.

3. Ihsan

Kyautatawa ko kuma muce kirki wato sunan na nufin aikatawa da nuna kirki ga jama'a.

4. Intisar 

Mai nasara ma'anar sunan kenan, wato yarinya wadda ake yiwa fata tayi nasara a rayuwarta.

5. Husna

Kyakkyawa wato yarinya mai kyau kuma da kyawun halaye.

6. Mufida

Me amfani ko kuma nace Mufeedat yana nufine ga mutum mai amfani da amfanarwa.

7. Amatullah

Ma'anar wannan suna shine baiwar Allah. Kuma muna yi mata zaton ta kasance ta gari.

8. Ahlam

Yarinya me kyakkyawan mafarki shine abinda ahlam a larabci yake nufi.

9. Saddiqa 

Wasu kuma suce Siddiqa duka dai suna nufin me gaskiya, iyayen da suka sakawa yarsu wannan sunan sunada burin diyarsu ta kasance mai gaskiya.

10. Sayyada

Shugaba yake nufi wato mace shugaba a cikin mutane.

11. Khairat

Sunane wanda yake nufin me alkhairi.

12. Afaf 

Kamammiya wato mace mai kamewa daga halayen banza na rashin kirki da kuma kamewa daga haram.

13. Basmah

Sunan kusan yana matukar tashe a wannan zamani yanzu, kuma yana nufin murmushi a ma'anarsa.

14. Nasreem

Ma'anar wannan suna shine fure ko fulawar aljanna me ƙamshi.

15. Salima

Mace me aminci wato yana nufin amintacciyar mace wacce keda riƙon amana a rayuwarta.

Mu al'ummar Hausawa muna daga cikin mutane masu Sa'a domin kusan yawancinmun al'adunmu addinin musulunci ya aminta dasu. 

Kamar yadda ubangiji Allah ya nufa mun kawo ƙarshen wannan bayani namu na sunayen mata da ma'anarsu. A huta lafiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post