Yaku mata a cikin wannan rubutun zan yi taƙaitattun bayanai a game da gashin kai, muhimmancin sa, muhimmancin gyaran sa a tare da haka da bayanai kuma akan yadda zaku gyara gashin ku da karkashi, ruwan shinkafa, ganyen magarya, albasa, aloe vera, man shanu, wiwi da man zaitun. Sai ku matso ku bani hankulan ku domin karanta abinda rubutun nan ya ƙunsa wanda akayi tata akayi rairaya aka kawo muku shi domin amfanin ku.
Gashin kai dai ba domin kwalliya kawai yake a kanmu ba, yana bayar da kariya ga fatar kai watau scalp daga saurin samun rauni a lokacin hatsari ko buguwa haka kuma da zafin rana ko kuma ɗumama kai watau warmness a lokacin da ake tsanananin sanyi.
Gashin kai watau scalp shi ya fi komai yawa a duka ire iren gashin da ake iya samu a jikin ɗan adam.
Gashin kai yana bayar da kariya a lokacin zafi da kuma sanyi wajen samarwa da ƙoƙon kai yanayin ɗumama lokacin sanyi , kuma yana bayar da kariya daga saurin samun ƙananan raunuka.
Gashin kan mutum kuma yana ƙara fito da kyawun surar ɗan adam walau mace walau namiji, saboda haka ko a iya waɗannan dalilan aka tsaya zaku ga cewa kula da gyaran sa da kuma inganta shi wani abu ne da yake wajibi a garemu. Akwai hanyoyi da dama da mace zata iya bi tayi amfani dasu domin gyaran gashin kanta ko da bata kai ga zuwa saloon mai tsada tayi wasa da kuɗaɗen ta domin a gyara mata shi ba. A cikin ire iren hanyoyin da za'a bi domin gyaran gashi mai inganci za'a yi amfani da abubuwa ne da ake amfani dasu na yau da kullum a cikin gidajen mu wanda suka kasance abubuwa ne na cima. Gasu kamar haka;
-Karkashi
-Ruwan shinkafa
-Ganyen magarya
-Albasa
-Aloe vera
-Man shanu
-Wiwi
-Man zaitun
Yadda ake gyaran gashi da karkashi
Karkashi wanda ake kaɗa miyar tuwo dashi watau miyar nan mai yauƙi kar kuyi mamaki don kunga na ambato shi cikin gagga gaggan ababen da ake gyara da inganta gashi dasu. Hakan ya samo asali ne saboda bincike na masana da manazarta sun tabbatar da alfanun sa wurin kashe cututtukan fatar ƙoƙon kai watau scalp waɗanda suka haɗa da amosanin kai, makero da irin su kwarkwata.
Yadda ake amfani da karkashi kuwa shine za'a samu ruwan zafi sosai sannan a kawo garin karkashi a zuba ya jiƙu sosai. Bayan ya jiƙu sai ki jiƙa gashinki a cikin ruwan karkashin na kamar tsayin mintuna talatin. Za'a iya yin wannan sau biyu a sati domin samun cikakken sakamakon da ake so.
Yadda ake gyaran gashi da ruwan shinkafa
Wannan ruwan da aka wanke shinkafa da shi ake kuma zubarwa yau da kullum yana da sinadarai masu yawa dake ƙara wa gashi tsayi, kyau da kuma laushi. Ko da ba'a faɗa ba ruwan da ake wanke shinkafa da kuma ruwan da ake tace shinkafa daga cikinsa bayan anyi parboilng ɗinta ɗauke yake da starch mai yawa a cikinsa, shi kuwa starch cike yake da sinadarai masu bawa hair follicle garkuwa.
Yadda zaki yi shine zaki wanke gashinki da ruwan shinkafa sau ɗaya a sati domin samun wannan kyakkyawan sakamako.
Ga matakan da za ki bi daki daki domin wanke gashinki da ruwan shinkafa kamar haka:
Ki samo shinkafa mai kyau, kofi ɗaya ma ya wadatar ko kuma duk yadda kike so ta zama. Sai ki zuba wa shinkafar ruwa ki bar ta ta jiƙu na tsawon minti 20 zuwa 30. Ki riƙa yawan juya shinkafar saboda kar ta dunƙule. Idan ruwan ya koma launin ruwan madara alamun starch ɗin ya samu zama a cikin ruwan kenan, to hakan na nuna cewa ya yi yadda ake so.
Daga nan sai ki tace ki raba ruwan da shinkafar. Sai ki jiƙa gashinki a cikin ruwan, in zai yiwu ki bar shi ya jiƙu na kamar minti talatin zuwa arba'in.
Bayan haka sai ki wanke gashinki da ruwan sanyi ki taje shi har sai kin tabbatar duk wani abun shinkafar ya fita daga kanki. Daga nan sai ki ɗaure gashinki. Idan kika jiɓanci yin wannan ina mai tabbatar miki da cewar zaki ga abin mamaki.
Waɗannan su ne matakan da za'a bi daki daki domin jiƙa gashin kai da kuma wanke shi da ruwan shinkafa.
Yadda ake gyaran gashi da ganyen magarya
Idan kika tashi gyara gashinki da ganyen magarya to zaki nemo ganyen magarya sai man zogale da kanunfari kaɗan a matsayin mahaɗin sa.
Za'a daka ganyen magarya a haɗa da man zogale da kanunfari kaɗan a ɗinga shafa wa gashi shima wannan haɗin yana gyara gashi sosai, yana ƙarawa hair follicles lafiya da garkuwa daga duk wani abu da zai kawo musu cikas a lafiyar su.
Haka kuma kamar yadda na faɗa a wasu rubuce rubucen masu alaƙa da wannan yawaita cin waɗannan kayayyakin yana ƙara kaurin gashi da yawansa da cikar sa sannan kuma yana ƙara baƙin gashi.
Yadda ake gyaran gashi da albasa
Saboda yanayin tsayin lokacin da gashi ke dauka wajen taruwa a wurin wasu mutane da yawa. Wannan ne dalilan daya sa zaku ga mutane da yawa basu fiye bawa gashin nasu muhimmanci ba. A cikin wannan rubutun zan kawo muku jerin hanyoyi na kulawa da gashi ta hanyar yin amfani da ruwan albasa saboda bincike ya tabbatar da sinadarai ma su matuƙar amfani a gashin ɗan adam musamman na kai.
Yin amfani da ruwan albasa yana matuƙar taimakawa wajen inganta ƙoshin lafiyar gashi, tare da yaye wasu cututtukan gashin da kuma fatar kai.
Albasa tana inganta lafiya da yalwa tare da haɓaka fitowar gashi a jikin ɗan adam a sanadiyar sinadarin da yake taimakawa wajen narkewar kwayoyin hydrogen peroxide masu inganta lafiyar gashi.
Yana taimakawa wajen inganta kwayoyin hair follicle na cikin gashi waɗanda suke ƙunshe da sinadarin sulfur. Sulfur kuwa a gashin ɗan adam tamkar taki ne a gona, ya na kuma hana sirancewar gashi da hana karyewar sa.
Sinadarin antioxidants suna tallafawa wajen hana fitowar furfurar gasu da wuri. A sakamakon sinadaran antibacterial na cikin ruwan albasa, su na taimakawa jijiyoyin gashi wajen kariya daga cututtuka musamman amosani tare da inganta ƙoshin lafiyar su. Haka kuma yana inganta zagayawar jini a cikin jijiyoyin gashi ta hanyar inganta kwayoyin follicle na cikin kai.
Za ki samu ɓawon albasa, albasa dai wadda ake amfani da ita a girki a matsayin spices to ɓawon ta na baya wanda ake zubar da shi, sai ki samu fry pan watau pan na suya ki zuba wannan ɓawon albasar a ciki sai ki ɗora shi a wuta amma wuta kaɗan za'a saka masa saboda kar ya ƙone sai ki riƙa juya shi sama-sama har ya yi baƙi shi ne ya soyu idan ya yi baƙi sannan ki sauke shi ya ɗan huce, daga nan ki samu turmi mai kyau ki daka shi ya yi laushi, sai ki samu abin zubawa ki zube shi sannan ki kawo man albasa ki zuba sai man hulba shima ki zuba, sannan man habbatussaudah shima ki zuba, sai nescafe ɗinki shima za ki iya daka shi ko niƙa shi saboda ya yi laushi.
Bayan kin daka shi shima sai ki haɗa su duka ki gauraya gaba ɗaya ki kuma samu kwalba irin ta man kitso ko juye a ciki. Wannan haɗin shi zaki mayar man kitsonki. Kuma ko ba kitso zaki yi ba ki jiɓanci amfani dashi a gashin kanki to tabbas zaki ga abin mamaki domin gashinki zaiyi wata irin cika ta ban mamaki haka kuma yana maganin amosani na kai da sauran matsaloli.
Yadda ake gyaran gashi da aloe vera
A samu ‘aloe vera’ a matse ruwan sa sai a haɗa da man zaitun a kwaɓa su, su kwaɓu sosai sannan a riƙa shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai. Yin haka na sa baƙin gashi da kuma dada masa tsawo da ƙarfi. Haka kuma yana sa gashin kai ya ciko yayi kauri sosai.
Yadda ake gyaran gashi da man shanu
Amfani da man shanu akanki yana buƙatar sai kin fara tsefe gashin kanki kin taje shi sosai, sai ki ɗakko man shanun ki riƙa tsaga gashin kina shafawa haka za ki yi kamar yadda ake shafa man kitso har ki game kan gaba ɗaya, sannan sai ki riƙa shasshafawa jikin gashin sai ki ɗaure gashin, sannan ki samu hula ki sa ki barshi ya yi kamar awa ɗaya zuwa biyu sai ki wanke za ki ga yadda gashinki zai zama. Ta wannan hanyar idan kika jiɓanci amfani da ita tana kawo yalwar cikar gashin kai.
Yadda ake gyaran gashi da wiwi
Wiwi dai kamar yadda kowa ya sani wata taba ce da ake zuƙa ake kuma cakewa ko nace buguwa idan aka sha ta. Amma kuma tabbas ko a cikin masu amfani da baƙar tabar watau wiwi, zaku ga gashi yana saurin fito musu a sassan jikinsu ba don komai ba sai don wanzuwar sinadaran da suke saurin haɓaka fitowar gashi suke kuma inganta lafiyar sa, bincike ya jima da tabbatar da hakan.
Idan aka samu iri watau seeds na tabar wiwi sai a dake shi ya zama gari sai a zuba shi a cikin man kitso a cakuɗa, a haka za'a riƙa amfani dashi.
Yadda ake gyaran gashi da man zaitun
Man zaitun yana da matuƙar amfani sosai, saboda yana ɗauke da sinadaran da ke ƙara wa gashi ƙoshin lafiya. Yana ƙarawa gashi tsayi da cika, ya hana bushewa ko zubewar gashi, sannan ya kashe amosanin kai, ya sa gashi laushi, ya ƙarawa matsirar gashi ƙarfi.
Kwaɓin man zaitun da tafarnuwa na ɗauke da muhimman sinadaran da gashi ke buƙata, irinsu selenium, vitaminC, omega 3, omega 6, antimicrobials, oleic acid, kitse, mai da ba shi da karfi, sulfur, antioxidants, bitamin E, bitamin K.
Idan gashinki mai zubewa kuma kina so ya daina kuma yayi tsawo, sai ki yi amfani da haɗin man zaitun da tafarnuwa domin yin hakan zai sa gashin ya daina karyewa sannan kuma ya samu lafiyar tsirowa daga matsirar sa.
A samu man zaitun sai a niƙa tafarnuwar sosai a sa a ciki, a bar haɗin ya yi kwana huɗu. A riƙa amfanin da kwaɓin a rufe gashi, sai a sa tawul mai zafi a rufe a bar shi na tsawon awa biyu. Daga nan sai a ruwa mai ɗumi a shamfo da conditioner a wanke domin kashe warin tafarnuwa.
A maimaita hakan sau biyu a mako daya.