Yadda ake tsara budurwa farkon haduwa

Yadda ake tsara budurwa farkon haduwa
Yadda ake tsara budurwa farkon haduwa 

Tsara budurwa kamar yadda duk wani saurayi ya sani "is not a work in the park".. watau yana nufin ba abu bane mai sauƙi. Kowace mace kamar sauran mutane ce, saboda haka tana da nata tunanin, haka kuma tana da nata dabi'un kaga kenan yadda zaka tunkari wannan budurwar yana da bambanci da yadda zaka tunkari waccan budurwar. Haka kuma, zai iya zamana wannan budurwar mai sauƙin sha'ani ce yayin da waccan takasance mai wuyar sha'ani, wata budurwar mai aji ce, wata mai yawan yanga, wata tana da raini, fankama da ɗagawa haka kuma zaku ga wata gata nan dai sam babu class watau aji. 

Idan kayi la'akari da lissafe lissafen nan, to za kaga cewar yadda zaka tsara budurwa wani fanni ne mai zaman kansa, ba kowane namiji bane ya iya bi da mata kala kala ta yacce yake so ba, da yawa kuma daga cikin maza ma basu iya tunkarar mace ba, ire iren mazan nan daza kuji ana kira ko yiwa laƙabi da "liverless" waɗanda suke shayin yiwa mata magana. 

Babu shakka mace na da wuyar sha’ani muddin ba a gano lagonta ba, amma daga lokacin da aka gano lagonta shi kenan sai kuma a fahimci ai sauƙin sha’ani gareta.

Haka suma maza da dama daga cikinsu akwai su da wuyar lamari da ganewa.

Akwai tarin hanyoyin da ake bi wurin tsara budurwa, za ma ta iya yiwuwa ka san mafi akasarinsu, kawai dai ba ka taɓa gwadawa ba ne, ko kuma kana shakkar gwadawa.

Zamani yazo da wani irin juyin-juya-hali ta kowacce irin fuska, abin kuma har cikin soyayya ya shiga ciki.

Waɗansu mutanen har yanzu sun yi matuƙar amanna da cewa, soyayya ta gaskiya (wacce ba don kuɗi ake yinta ba) har yanzu tana raye a ban ƙasa.

Yayin da kaso mafi yawa cikin mutane ke ganin soyayya ta gaskiya yanzu sai ɗaiɗaiku ke dacewa da ita, amma muddin kana da wuri to kafi masu wuraren zuwa dace.

Ba zan yi mamaki ba, in har kowanne tsagi na waɗannan nau’ikan mutane ya tsaya a matsayarsa.

Domin kowa da ra’ayinsa, kuma mu ganau ne a fannin soyayya ba jiyau ba.

Shin akwai so na gaskiya har yanzu?

Kwarai_da_gaske_soyayya_ta_gaskiya_wacce ake_yinta_tsakanin_ruhi-da-ruhi_har_yanzu akwai_ta.

Sai dai ɗaiɗaiku ne daga cikin mutane ke yin dace da samun irin wannan soyayyar. Soyayya ce mai kyau sai dai kuma tana matuƙar wahalar da masu yinta.

Ta ya zaka tsara budurwa a haɗuwarku ta farko 

A nawa tunanin, tsari da kuma sace zuciyar budurwa kusan abu ɗaya suke nufi. 

Amma, shi tsara budurwa na buƙatar iya kalaman soyayya masu matuƙar ratsa zuciya, da kuma dakewar zuciyar iya tunkarar wacce ake so.

In har da hali, ka haɗa da ƴar ƙarya-ƙarya ba laifi bane, ka bayyana wa mace irin son da kake mata cikin tausasa murya.

Anan fa ba wai ina nufin ka samu ƴar mutane kayi ta zumbuɗa mata ƙaryar kana da kuɗi ko wani abu ba. A'a kar kayi haka sam. Anan ina nufin kaɗan haɗa mata da ƙaryar irin son da kake mata, ina nufin kayi exagerating watau ka koɗa irin son da kake mata. Irin misalin ka riƙa ce mata itace bugun numfashinka. 

Saboda kana son mace, kada ka tsaya ta rinƙa wankarka, ko kuma ta mayar da kai garan ƙauye wanda bai san me yake yi ba.

Ka rinƙa kyautata mata, domin zuciya na son mai kyautata mata, kuma ka kasance cikin tsafta a kowanne lokaci.

Har_ila_yau, tsara_budurwa_baya_wahala in dai_kayi_nasarar_yi_mata_magana_ta tsaya ta_saurareka_muddin_kana_da_bakin maganar.

Tsari_fa_ko_a_ina_ne, ba'a iya_fagen_soyayya ba, zance_ne_daki-daki mai_ma’ana.

Don haka, sai ka tanadi kalamai na musamman domin tsara wacce kake so.

Yadda ake sace zuciyar budurwa

Karfa kaji nace sata, kai fa ba ɓarawo bane, saboda haka bana tunanin akwai wata hanya wacce zaka sace wa budurwa zuciya.

Illa iyaka dai, zata faɗa kogin soyayyarka in har kayi iya iyawarka wurin bin waɗannan hanyoyin guda takwas da zan jero maka yanzu.

Tsari

Anan ina nufin kamewa. 

Ka zama mai tsari a rayuwa. Anan tsarin da nake nufi shi ne; tsari na sanin ciwon kai, sanin ya kamata, ba rashin kan gado ba da kuma tsarin rayuwa mai kyau bana magana ba.

Mace na son yin mu’amala da namiji wanda yake mai tsari, komai nasa a tsare.

Haƙiƙa, da za kayi ƙoƙari ka fara tsara rayuwarka, da mu’amalarka (da maza da mata) lallai ko da duk wacce tayi nasarar samun soyayyarka ta matuƙar dace.

Kyau da Kwalliya

Kamar yadda yatsunmu basu kasance ɗaya ba, to haka kyawunmu, dirinmu da zubin halittarmu basu zama ɗaya ba. Haka kuma ba zasu taɓa zama ɗaya ba. 

Waɗansu matan da yawa na son yin soyayya ko tsayawa da saurayi ɗan gayu, kyakkyawa (daidai gwargwado har ma fiye da haka) wanda ya san wanka da kwalliya.

Shi yasa sau tari za kaga mata na yin soyayya da saurayi. Ka rasa me yasa, in kayi duba da kyau, za kaga ko dai yana da tsari, ko yana da kyau ga iya kwalliya kamar ɗawisu.

So dai kowa ya sani makaho ne, abinda yayi maka, sai kaga bai yi wa wani ba.

Kalamai

Kalamai sune daman abinda wannan rubutun ya ƙunsa, kuma muna magana ne akan yadda za'a sace zuciyar budurwa. Kaso tamanin  ko casa'in na irin ƙoƙarin da saurayi zaiyi ya sace zuciyar budurwa sun ta'allaƙa ne akan kalamai kawai, ragowar kaso goman kuwa sune duk wani ƙoƙari da dabarun dazai iya haɗawa dasu wurin ganin ya samu nasarar sace zuciyar. 

Yana da matuƙar muhimmanci namiji ya iya kalaman soyayya masu zafi, waɗanda zasu riƙa kwantarwa da mace hankali, su sanyaya mata rai, su kuma sanya ƙaunarsa cikin zuciyarta.

Akwai samari da dama waɗanda dalilin rashin iya kalamai masu daɗi ya sanya suka rasa soyayyarsu (wani ya musu kwace).

Shi yasa ya kamata ka iya kalaman soyayya, ka naƙalcesu yadda ya kamata. 

Kulawa da Kirki

Zuciya na son mai kyautata mata, don haka yana da matuƙar amfani ka riƙa kulawa da budurwarka yadda yakamata.

Ka riƙa yi mata abubuwa waɗanda zasu riƙa sa tana ganin kirkinka.

Kulawa ta haɗar da taƙaita chat ta WhatApp da call, ku rinƙa haɗuwa da yammaci kuna zantawa baki-da-baki.

Kana yi mata murmushi mai cike da alƙawari da ƙauna, itama tana yi maka.

Sakamakon haka zata riƙa ganin kana kulawa da ita kwarai da gaske, madadin ka uzzura mata da chat a WhatsApp.

Barkwanci

Sufa mata da kuke gani ƴan nishaɗi ne, wannan kowama ya sani, saboda haka kar kayi mamakin don ganin barkwanci a cikin jiga jigan hanyoyin daza kabi ka sace zuciyar wadda kake so. 

Inda son samu ne, kada ka riƙa yiwa budurwarka barkwanci kaɗai yayin da kuke yin waya ko chat.

Duk lokacin da kaje wurinta domin kuyi hirar soyayya, ka rinƙa dan takalarta da barkwanci, kuna yin raha.

Hakan na matuƙar ƙara danƙon soyayya.

Kyautatawa

Kyautatawa na nufin yin kyauta. 

Akwai mutumin da baya son kyauta kuwa? I don't think so. Kowane mahaluƙi yana son kyauta, haka kuma kowane mahaluƙi yana jin daɗi da farin ciki idan aka kyautata masa. 

Saboda haka rashin alkhairi da kuma rowa basu da wurin zama a soyayya. Ku riƙe wannan. Take note ! 

Haka kuma akwai matan da suma halinsu ɗaya da mazan wurin rowa, da kwaɗayin tsiya.

Ya kamata, kai a matsayinka na namiji ka rinƙa yawan kyautatawa budurwarka akai-akai.

Kamar su kyautar kuɗi inka samu dama, da ƴan abubuwa dai haka. Kai duk abinda ka san zai sanyata farin ciki muddin ka siyo mata shi ko kuma ka bata shi, to kayi, saboda soyayyarka ta ƙara damƙe zuciyarta.

Ke kuma, saboda ya saba baki, hakan ba shi zai sa ki matse hannunki gam ba, sai dai ki karɓa amma baki bayarwa ba.

Ki riƙa yiwa saurayinki ƴan ƙananun kyaututtuka, hakan zai sanya yaji a ransa cewa, eh lallai kina ƙaunarsa kuma ke ɗin ta daban ce.

Bari kaji yadda abin yake ; A matakin farko kana buƙatar ka san abinda yake burge ƴan mata da kuma abinda suke so tukunna. Kwantar da hankalin ka kaji. Kaa ga! duk ba maganar ƙoƙarin ka a makaranta bane, ko sai mahaifinka ya zama wani sannan a soka. Daɗina da kai gajen haƙuri! Nace maka ba sai kayi dagiya ka sayi mashin ko mota ba. Zata bika ta soka, kuma ta mato a soyayyarka muddin kabi wannan taswirar watau blue print ɗin da kake karantawa. 

Amma kafin ka tunkareta ya kamata kasan waɗannan sharuɗan kamar haka;

-Mace bata son matsoraci ko wanda ya cika fariya ko mai girman kai.

-Mata basa son namiji mai yanga duk sai yabi ya gundure ta,  kana yanga tana yanga me kenan akayi?

-Mace tafi son wanda baya jin kunyar fada mata duk wani motsin sonta dake zuciyar sa

– Mata basa son hauragiya da harigido, saboda haka ka natsu ka fuskance ta.

– Mace tana son namijin da yasan darajar mata, kaga kenan kar ka kuskura ka bata labarin cewa wai mata da yawa suna sonka amma ka wulaƙanta su saboda ita da zarar taji haka to kashin ka ya bushe koda ta amsa tana sonka,

-Sannan kar kaje kai tsaye kace ‘Ina sonki’ ai sai ka firgitata, ana buƙatar abin nan da turawa suke kira ‘Introduction’ kaga zaka tanadi ƴan bayanai masu ma’ana kenan wanda suka dace da ita domin ba sakin baki zakayi ka rinƙa zuba kamar kanyar da ba daɗi ba.

Kuma ka nuna mata kasan darajar kanka, don haka kar ka kuskura ka roƙeta ta soka sai ta raina maka wayau, ko kuma taja maka aji sosai kafin idan kaci sa’a ta amince, idan kuma ba’ayi sa’a ba to kuma abin dai ba’a cewa komai.

Sanin kowa ne jin daɗin rayuwa sai mutum ya sami irin macen da yake so sannan zai gane a daɗi yake ko a wahala. Ta yaya zaka shawo kan macen da kake so ka rayu da ita?

To dakata! Ita dai mace da kake gani, daga ƴar shekara 1 zuwa 100, ma’aunin tunaninsu ɗaya ne. Harshenka da kwakwalwarka, makamai ne masu ƙarfin da har yau mace bata mallaki garkuwar kare hare harensu ba. Idan kana so ka sace zuciyar budurwa da kalamai, waɗanda zasu ratsa ta duk jikinta ya samu tabbataccen wajen zama a zuciyarta ya zamana ba mai faɗa mata taji in bakai ba, koda kuwa iyayenta ne, to kuwa iya kalamai na nutsuwa masu nuni da zallan son da kake yi mata tare da haka kuma da gani kimarta a matsayin diya mace, kuma duk a cikin wadannan kalaman da zakayi mata ka hada da barkwanci a ciki to matukar taji su cikin bayanan ka da kake mata. 

Mace tana so taji irin waɗannan kalamai ta bakin duk namijin daya tsaya a gabanta domin neman soyayyarta. Kuma dayawa daga matan basa gane ya akai ka iya sace mata tunani da zuciya. Karkayi ƙasa a gwiwa, da kaga mace kana so kai tsaye ka tunkare ta ba da wata fargaba ba. Kana zuwa, dama fuskarka a sake take kamar kaga na gida. 

Daka gabatar mata da kanka to karka tsaya wata inda-inda saboda ai itama yarinyar dole tasan dalilin da zaisa ka tare ta ba komai bane illa neman soyayyarta. 

Kubi taswirar nan a sannu domin sace zuciyar budurwar da kuke so kuke mafarkin samu!

Post a Comment

Previous Post Next Post