Yadda ake hada maganin mata

Yadda ake hada maganin mata
Yadda ake hada maganin mata

Magungunan mata ko kuma kayan mata watau aphrodisiacs kenan a turance, sinadarai ne da aka tanada don ƙarawa mata sha'awa, jin daɗin jima'i, sha'awar jima'i da ni'ima da sauransu. Gaba ɗaya dai a taƙaice yana sa kusanci da ƙarin sha'awa. 

Magungunan mata ana yin sune ko kuma samar dasu daga ƴaƴan itatuwa na halitta, tsire-tsire, kayan ƙamshi, mai, irin mai, ganye da abinci da sauransu.

Shahararrun kayayyakin kayan mata sun haɗa da;

-ayu
-Kunun aya
-Tsumi; wanda yake cakuɗe ne na ganyen kayan mata da nonon raƙumi mai inganci da ƙarfi.

Ayu

Ɗaya daga cikin mafiya yawan amfani da kuma ƙarfin kayan mata akwai gi*din ayu. Wannan yana sa namiji ya mannewa mace idan tana masa amfani dashi. A ɗabi'ance kamar yadda ayu wannan dabbar ta cikin ruwa yake mayen jima'i to kamar hakane ga ma'abota amfani da maganin mata gindin ayu. 

Gumba

Tana taimakawa jiƙewar farji kuma tana sa jima'i daɗi. 
Amfani: A samu wani kaso kaɗan daga kowane kalar gumba sai a haɗa su a kofi da madara ko kuma a sha awa biyu kafin jima'i.

Zumar mata

Ingantacciyar zumar da uwargida zata dawo da martabarta agurin maigida asami cikakkiyar gamsuwa dajin daɗi tana ƙara fahimtar juna da ƙaunar juna tare da jan hankalin maigida tana kuma taimakawa uwargida ta ɗinga samun kyauta da alheri agurin maigida.
Tana saukar da ni'ima sosai tana hana bushewa tare da samar da ɗanɗano mani'imci.
Ana haɗa tane daga tsirrai ingantattu masu ƙara lafiyar al'aura da kuma jiki.

Tsumin tabaje 

Da farko za'a wanke ɓaure a zuba a tukunya da wadataccen ruwa a barshi ya dahu sosai, sai a sauke a cire itacen a maida ruwan kan wuta a zuba kanunfari da mazarkwaila a rufe ya cigaba da dahuwa sai a sauke a tace a zuba a wani wuri asa a fridge ya ɗanyi sanyi, idan ya kwana dole sai an ɗumama saboda ɗanɗano zai canza saidai idan akwai fridge, idan za'a sha a zuba zuma a ciki.

Abebaɗai na kayan mata na matsi

Ana amfani da abebaɗai da yawa waɗanda suka danganci harkar yin matsi na mata. Cikin ire iren abubuwan da ake matsi dasu sun hadar da zumar mata, bagaruwa, kanunfari, magarya, kwallon tumfafiya da sauransu. 

Misali daga cikin irin haɗe haɗen da akeyi na matsi sune;

-Ana tafasa ruwan ƴaƴan bagaruwa da magarya a zauna a cikin ruwan zafi na kimanin mintuna talatin. 

-Ana yi matsi da haɗaɗɗiyar zuma wacce za'a riƙa lakata ana shafawa a farji safe da dare

-Ana yin tsarki da tsumammen ruwan kanunfari domin matsi da tsukewar gaba. 

Maganin mata na mallaka 

Maganin da mata suke amfani dashi domin mallakar miji ko saurayi nau'i nau'i ne. Kuma nau'in ya danganta da irin wurin wanda akaje wurinsa ya bada shi wannan maganin mallakar. Kamar misali idan mace ta tashi tana son maganin mallaka wanda za tayi amfani dashi domin mallakar namiji shi kaɗai, idan misali a cikin mata da yawa take kamar misali kishiyoyi kenan sau tari wasu matan kan samo maganin mallaka ne na laƙani ko na rubutu ko laya. 

Misalin budurwa ko bazawara masu son mallakar wani namiji sunfi amfani da maganin mallaka na hatimi, to koma dai wanne ne a cikin ire iren magungunan mallakar nan, zanyi bayanin su ɗaya bayan ɗaya kamar haka;

Maganin mallaka na laya;

Shi dai wannan nau'in maganin ko lakanin mallakar da yake zuwa ta sifar laya ko layu, da farko dai akwai buƙatar mu fahimci menene laya ? 

Laya wacce a turance ake kira da talisman, wani ɗan ƙaramin dunƙulallen abune wanda a cikinsa yake ƙunshe da farar takarda wacce aka ninke aka kuma saka fata aka ɗinke ta. Ɗinkin da za'a yiwa wannan farar takardar kuwa ana amfani ne da jemammiyar fata wacce baduku zaiyi amfani da ita ya ɗinke. 

Ita farar takardar da aka ɗinke mai ta ƙunsa a jikinta ? 

Sau tari ita dai takardar laya wacce ake ɗinkewa, ana yin wani aiki ne a kanta kafin a kai ga layance ta, misalin ayyukan da ake yi akan farar takardar kuwa sune; wasu mutanen musamman malamai sukan yi rubutun ayoyi ne kawai ko kuma ayoyi tare da wasu addu'o'i ko kuma wuridai a jikin farar takardar sannan a linke a kaiwa baduku ya ɗinke ta. Wannan kenan. 

Sannan akwai nau'in layoyi da akeyi na sihirin mallaka ko kuma wani nau'in sihirin daban, a irin wannan nau'in layu ana amfani da ayoyi amma kuma ta hanyoyin da basu dace ba, misali anan kamar ayi rubutun aya a bai bai misali daga ƙarshen ayar zuwa farkon ta ko kuma a datse daga tsakiyar ayar zuwa ƙarshe sannan farko kama irin haka dai. Sannan kuma akan iya haɗa ayoyin da kuma wasu rubuce rubucen tsubbu kona surƙulle a haɗa a ninke a kuma bawa baduku ya ɗinke ta, wannan ma wani nau'i ne nau'in laya amma kuma wacce tasha bambam data farko irin wacce malamai keyi ko kuma suce ga yadda akeyin ta. 

Baya ga wannan kuma akwai nau'in layoyi da akeyi wanda basa ɗauke da ayoyi sai dai rubuce rubuce na tsubbu misali waɗanda suke ɗauke da sunayen aljanu da hatiminsu ire iren layoyi kenan da ƴan bori suka fi amfani dasu. Duka irin nau'in layukan nan ana amfani dasu da niyyoyi daban daban kamar dai misalin layar da aka haɗa domin mallaka. 

Maganin mallaka na rubutu;

A wannan nau'in maganin ko kuma laƙani na mallaka shine wanda za'a yi rubutun wasu ayoyi a allon sha ko kuma wata farar takarda sannan a wanke, ruwan da aka wanke wannan rubutun dashi, shine za'a bi ta wasu hanyoyi daban daban domin yin amfani dashi. Misalin maganin mallaka na rubutu wanda mata suka fi amfani dashi shine wanda idan akayi rubutun nan za'a wanke daga nan sai su ɗauki rubutun suna amfani dashi wajen yin girkin da zasu ciyar da namiji a abinci ko kuma suke haɗa wani abinsha kamar zoɓo ko kunun aya wanda a ciki zasu ke zuba wannan ruwan a yayin haɗa lemon ko kuma kunun duk dai da niyyar mallakar namiji ko kuma ƙudurin da aka kuɗurce a zuciya domin sa. 

Akwai nau'in maganin mallaka na rubutu wanda shi kuma a jikin wata sarrafaffiyar farar takarda ake yin sa. Ita dai wannan takardar fara ce a launin ta amma kuma sam bata da kauri ma'ana shafal shafal ce. Ita dai wannan takardar ana yin rubutu ne a jikinta ko dai a wanke ko kuma bayan anyi rubutun sai ayi turarensa da ita watau ta hanyar ƙona takardar. Wai hikimar yin turaren nan shine ayi amfani da hayaƙin da ƙonanniyar takardar ke fitarwa ya ratsa jikin mace sosai. Yawancin irin wannan nau'in, mace tana yi ne kafin ta kai ga tunkarar namijin da take son mallaka ko kuma namiji da akai mata wannan aikin akan sa ko kuma saboda shi. 

Maganin mallaka na hatimi;

Shi ma wannan nau'in maganin ko kuma laƙanin mallakar yana kama da nau'in rubutun sha ne wanda za'a yi rubutun hatimi a wanke, mace tayi amfani dashi wurin yin girkin da zata ciyar da namiji ko kuma kuma wurin haɗa lemon da zata shayar dashi domin mallakeshi. Haka kuma akan zana hatimi akan irin wannan farar takardar da nayi bayanin ta a sama. Idan akayi zanen hatimi sai a wanke shi mace ta sha ko kuma tayiwa namiji wani aiki dashi akansa ko kuma ita tayi sirace ta hanyar ƙona takardar nan domin hayaƙin ya ratsata, yadda dai za tayi da zanen hatimin nan ya danganta ne da yadda sharuɗɗan amfanin dashi yake ko kuma yadda aka gindaya mata. 

Mallaka na ɗabi'a;

Wannan nau'in hanyar mallaka na ɗabi'a shine wanda addini ko al'ada basu kore ba. Anan a kuma irin wannan nau'in hanyar mallakar namijin, mace zata yi amfani da ƙissa da kuma kisisinar tane domin janyo hankalin ɗa namiji zuwa gareta ne kaɗai ta yadda gaba ɗaya hankalin sa da kuma tunanin sa bama zai riƙa kaiwa ga wasu matan ba. Sau tari idan mace tana amfani da wannan hanyar za kuga ana zargin cewa wai ko ta mallakeshi ne ta hanyar asiri saboda tsabar yadda za'a a ga namiji ya sururuce akan mace. Abinda yake faruwa anan wanda mutane suka kasa ganewa shine; ita hanyar mallake miji ko kuma namiji ta hanyar ɗabi'a shine kamar yadda na bayyana ko kuma na ambata a sama cewar mace zata jiɓanci yin wasu kyawawan ɗabi'u ne ta kuma cuɗanya su da ƙissa da kisisinar ta irin ta ƴaƴa mata domin ɗauke hankalin miji ko kuma wani namiji da take so. 

Remember, 

"if you want something you find a way to get it, if you don't you find an excuse.. 

To kamar hakane fa ga macen data ga namiji take so ko kuma take son riƙe mijinta ko kuma mallakeshi ita kaɗai. Mutane basu san irin wahalar data sha wurin jiɓantar kyawawan ɗabi'un ba; kamar irin su 

-ladabi da biyayya, 
-yi nayi bari na bari wanda hausawa suke cewa ba aibu bane, 
-kyautatawa iyayen sa ko makusantan sa shi mijinta ko kuma namijin da take so, 
-yi masa kwalliya dayi masa girke girke masu nishaɗantar dashi. 

Duka wannan abubuwan dana lissafo idan mace ta kiyaye su ta kuma jiɓanci yiwa namiji su, to ko babu laya babu tsumi babu dabara ina mai tabbatar muku haƙanta zai cimma ruwa. 

Maganin mata na gargajiya

Magungunan gargajiya da mata ke amfani dasu a gargajiyance kuma tun ada can suna da yawa, amma wannan rubutun zai yi duba ne musamman akan waɗanda suka fi shafar matsalolin na mata. 

-Idon zakara

Idon zakara wata ciyawa ce watau shrub kenan a turance, mai gajeru ko kuma ƙananun ganyayyaki wacce kuma a baki take da zaƙi idan aka tauna ta. Ƴaƴan ciyawar idon zakara suna yanayi da ƴaƴan dawa sai dai ita kalar ƴaƴan nata ja da baƙi ne kuma suna kama da kwayar cikin idon zakara wanda babu tantama akan haka ne aka laƙabawa wannan ciyawar suna idon zakara. Ciyawar idon zakara tana yin magunguna da yawa yawan gaske amma dai mata suna jiɓantar amfani da ita ne a gargajiyance na abinda ya shafi kwanciyar aure ga matan. Ana iya tafasa ganyen idon zakara asha cikin shayi ko kuma a daka a haɗa shi cikin kayan yaji. 

-No*non kurciya 

Ita ma dai wannan ciyawa ce amma kuma ita yaɗo take yi a ƙasa kuma ganyen ta kore ne, tana kwanciya a ƙasa inda danshi yake. Tana maganin ire iren cututtuka da ake ɗauka yayin saduwa. Ana busar da nonon kurciya sai a riƙa zuba garin a cikin nono ko ruwa ana sha. 

-Wuyan damo

Yana maganin ciwon mara, matsalolin zuwan jinin al'ada da sauransu

-Takalmin binta

Wani tsiro ne mai fitowa kala kala, amma mafi yawanci kore ne mai ɗauke da jar fulawa akan sa, yana kama da ƙasan takalmi. Yana maganin ciwon nono. 

-Fasa kumburi na mace

Yana maganin zubar jini, ciwon mara da cututtukan da ake ɗauka yayin kasanci.

Post a Comment

Previous Post Next Post