Wannan rubutun zai amsa muku jerin tambayoyin ku kamar; "Mene ne mafi kyawun samfuran wayar hannu?" Manufar wannan rubutun shine don samar da cikakken bayani kan jerin manyan samfuran wayar salula, menene kuma farashin su, haka kuma duk a cikin wannan rubutun za ayi duba kan yadda za'a magance matsalar mutuwar baturin waya da kuma matsalolin shan cajin wayar, tare da haka za ayi duba kan matsalolin screen, speaker da irin su charging point.
Ana samun manyan samfuran wayar hannu a kasuwanni a cikin shaguna, suna bai wa masu siyayya damar zaɓar mafi kyawun zaɓi domin amfanin kansu da dana ƴan uwa. Siyan wayar hannu wacce ta fi dacewa da mai buƙata shine mafi dacewa.
Wayoyin hannu da suke da tsada da yawa mafi akasari sune wayoyi masu wahalar sarrafuwa, ma'ana ba kowane yake iya sarrafa su ba, sau tari mutum zai iya siyan waya ya riƙeta na tsayin lokaci kuma har ya kai ga rabuwa da ita ba zai gama gano wasu daga cikin features na wannan wayar ba. A yayin da wasu wayoyin suke da wahalar sarrafuwa a hannu ɗaya, a wani hannun kuma akwai wayoyi waɗanda zaku same su suna da durability watau ma'ana suna da kwari ko kuma za'a iya cewa sassan jikin wayar yana da aminci domin kuwa bincike ya nuna wasu kamfanunnukan wayoyin sun fi wasu kwari da aminci. Wasu wayoyin ko ɗan yaya suka suɓuce suka faɗi to shikenan kuma daga nan sai fashewar screen da gocewar charging point da dai misalan sauran matsalolin da ka iya biyo baya, amma kuma wasu wayoyin zasu faɗi kuma kuga garau ba suyi komai ba, duk kuwa dai akwai tsautsayi wanda baya wuce ranar sa.
A tsawon lokaci, wayoyin salula su kan lalace, don haka yana da mahimmanci mutum ya samu wayar hannu mai dawwama wacce kuma ita ce tambarin mabuƙaci da aka fi so, tabbataccen alamar samfur mai inganci kenan wanda mafi yawan mutane sun shaida cewa wannan samfurin ko kuma wannan brand ko kuma wannan kamfanin wayar mai inganci ne. Farashin samfuran wayar hannu na iya bambanta, ya danganta da kayan da ake amfani da su da kuma ɗorewar samfuran, amma masu yin manyan tambarin wayar hannu suna da abin da ya fi dacewa ga masu siye. Masu ƙera wayoyin hannu sukan ƙera samfuran su don zama mafi kyawun amfani da gida (da kuma wasu samfuran wayar hannu mafi kyawun balaguro), kuma wannan mafi kyawun ƙima na jerin gida zai sanar da ku waɗanne ne cikin waɗannan mafi ingancin wayar hannu.
Mutane da yawa suna da zaɓi ko tambarin wayar hannu da suka fi so, suke siya kuma suke amfani dasu kuma wannan jeri ya ƙunshi duk sanannu, kuma amintattun samfuran wayar hannu da ake samu a kasuwa a yau. Kowannensu yana da'awar bayar da mafi yawan amintattun wayoyin salula a kasuwa, amma wannan shine abin da masu amfani da gaske ke ba da shawarar, dangane da zaɓen manyan samfuran wayar salula da ake samu a yau. Yana da kyau a tuna cewa mafi kyawun samfuran wayar hannu ga mutum ɗaya na iya zama mafi muni ga wani, kamar dai yadda hausawa masu iya magana suke cewa ne; watau abincin wani, gubar wani ko kuma yadda bature yake faƴa da yake cewa; one man's food is another man's poison kuma dole ayi la'akari sosai da ra'ayoyin masu amfani da wayar hannu yana da mahimmanci don gamsuwar cinikin ku. Daga cikin sanannun samfuran wayoyin hannu watau wayar salula ko mobile phones ko kuma wayar tafi da gidan ka, manyan kamfanunka ko kuma brands da suke samar dasu a yau sun haɗar da;
Samsung
Apple
Huawei
Redmi
HTC
Xiaomi
Tecno
Infinix
OnePlus
Vivo
Motorola
Asus
Nokia
Oppo
Realme
Alcatel
LG
Lava
Sony
Lenovo
Acer
Honor
IQOO
A bincike da kuma tata da rairaya da akayi kafin wannan rubutun anyi amfani ne da shafin yanar gizo mai suna ranker.com domin gano waɗanne kamfanunkan ko kuma samfuran wayoyin hannu ne suka fi samun shaidar amintaka a sassa daban daban na duniya. A cikin wannan bincike ne aka tabbatar da cewa kamfanin wayar sadarwa na samsung sunfi kowane kamfanin samun lambar yabo a sassa daban daban na faɗin wannan duniyar da muke ciki a yau, sannan wannan mashahurin kamfanin na Apple watau iPhone da suke biyewa samsung sai kuma kamfanunkan Huawei, Redmi da kuma HTC sannan saura suka biyo baya.
Farashin wasu daga cikin fitattun samfuran wayoyin hannu a yau.
Kamfanin Samsung
-Samsung Galaxy A55 5G 8GB+128GB + Galaxy Fit 3. ₦620,050.00
-Samsung Galaxy A15 8GB RAM + 256GB ROM. ₦284,500.00
-Samsung Galaxy A15 5G 6GB RAM + 128GB ROM. N250, 000.00
-Samsung Galaxy A55 5G 8GB+128GB
N200, 000.00
-Samsung Galaxy A55 5G 8GB+256GB.
N180,000.00
-Samsung Galaxy A35 5G 8GB+256GB ROM N175, 000.00
-Samsung Galaxy A35 5G 6GB +128GB ROM N172, 000.00
Kamfanin Apple (iPhone)
-Apple iPhone 15 256GB ₦1,990,000.00.
-Apple iPhone 15 128GB. ₦1,770,000.00
-Apple iPhone 15 Pro Max 512GB. ₦2,995,000.00
-Apple iPhone 15 Pro Max 256GB. ₦2,590,000.00
-Apple iPhone 15 Pro 256GB. ₦2,390,000.00
-Apple iPhone 15 Pro 128GB. ₦2,190,000.00.
-Apple iPhone 16 Pro 128GB · ₦2,499,000.00
Kamfanin Huawei
HUAWEI MatePad Pro 12.6. NGN 450,000.00
HUAWEI P50 Pocket 12GB+512GB. NGN 912,500.00
HUAWEI P50 Pocket 8GB + 256GB. NGN 850,000.00
HUAWEI NOVA Y61 4GB+64GB. NGN 120,000.00
HUAWEI NOVA 8i 8GB+ 128GB. NGN 221,000.00
HUAWEI NOVA Y70 4GB+128GB. NGN 155,000.00
HUAWEI Nova Y90 8GB+128GB. NGN 220,000.00
HUAWEI Band 7. NGN 55,000.00
Kamfanin Redmi
Redmi Note 12pro +5G. N424,000.00
Redmi Note 12pro [8+256] N307,000.00
Redmi Note 12pro [8 + 128] N292,000.00
Redmi Note 12pro [6GB + 128] N274,000.00
Redmi Note 12 [8GB+128] N191,000.00
Redmi Note 12 [6GB+128] N184,000.00
Redmi Note 12 [4GB + 128] N177,000.00
Xiaomi Redmi Note 11s 6/128GB N155, 000.00
Yadda za kayi matsalar shan cajin wayarka
Da farko dai yana da kyau idan an saka waya a caji kar a riƙa amfani da ita tana daga jikin cajin indai ba wani abu bane na hanzari watau emergency ya taso, domin kuwa hakan yana kashe battery yana kuma kawo matsalolin cajin waya daban daban. Haka kuma idan za ayi amfani da caja watau daga kan cajar ma'ana ɗan ƙundun nan ko kuma adapter a turance da kuma ita kebil (cable) a tabbatar duka original ne kuma musamman anfi son wanda yazo daga kamfani.
Matakin farko daya kamata abi wurin bincikar matsalar cajin waya shine kebul ɗin ku, adaftar da kuma ƙarfin wutar lantarki. Ayi ƙoƙarin yin cajin wata na'ura tare da adaftar wutar lantarki da kebul ɗin ku. A bincika cewa an haɗa kebul ɗin amintacce zuwa adaftar da kuma wayar.
A gwada cajin wayarka tare da wata kebul ko adaftar wuta domin jarrabawa ko taka kebil ɗin ke da matsala. Idan anga korayen haske, batirinku ya cika. Idan hasken ja yana walƙiya, babu isasshen wutar da za a kunna. Cajin wayarku na aƙalla mintuna 30 kafin a sake farawa. Idan baku ga gunkin baturi ko jan haske ba bayan kun kashe wayarku, matsalar na iya kasancewa tare da allonku watau screen.
Gumakan baturi da fitilu na iya bambanta ta waya. Don cikakkun bayanai na wayarku, sai ku tuntuɓi mai ƙera na'urar ku.
Yadda za kayi maganin matsalar fashewar screen
Hausawa suna cewa rigakafi yafi magani. Kamar yadda bature yake cewa prevention is better than cure kenan. To kamar haka ne a matsalar fashewar screen na waya. Idan ka samu wayarka yi ƙoƙari ka saka mata screen guard watau mai bawa screen kariya kenan, kaga kenan screen ɗinka ya samu kariya ko kuma zai riƙa samun kariya a yayin duk da tsautsayi ya gifta. Sai dai kuma a wata faɗuwar da wayar hannu zata iya yi, daga screen guard har ainihin screen duka zasu iya fashewa, to anan ne kuma indai har tsautsayin daya auku ya ɓata screen to kuwa sai an haɗa da canja wani sabo ko kuma ayi wa mutum dabara a kasuwar waya a yanka masa wani wanda bai kai na kamfani tsada ba.
Yadda za kayi maganin matsalar lalacewar charging point
Kafin a kai ga matsalar charging point da gyaran sa zanyi bayanin yadda zaku kiyaye lalacewar sa. Idan har kuna so charging point ɗinku yayi ƙarƙo kar ya riƙa samun matsala, a lura kuma a guji saka masa gindin charger wacce ta matse shi sosai har ya kai ga ana turawa da ƙarfi. Haka zalika a guji fizgo charger daga jikin charging point yayin da aka tashi cire waya daga charger daga charging point domin duka waɗannan halaye biyun suna matuƙar taimakawa wurin lalacewar charging point. Idan kuma charging poing ya lalace ma'ana ya mutu to dole ne sai dai a canja wani, kuma yayin da aka zo canja wa a tabbatar an saka original na kamfanin wannan wayar.
Yadda za kayi maganin matsalar lalacewar speaker
Idan har ba'a son samun matsalar speaker to a guji sanya abubuwa masu tsini kamar bakin allura a speaker a kuma guji busa iska da zubar ruwa a wurin speaker. Haka kuma idan ana danne sashen speaker wannan ma yana taimakawa sosai wurin samun matsalar speaker. Idan speaker ta lalace ana iya gyaranta idan kuma ba zata gyaru ba to tilas sai an haɗa da canza ta.
Yadda za kayi maganin matsalar rashin network.
Rashin network dai a waya akasari ba laifin wayar bane ba, matsalar rashin network ko ɗaukewar sa, ko kuma network ya riƙa kawowa yana kuma ɗaukewa ma'ana watau ya riƙa yin rawa yana fluctuating kenan a turance, wannan matsalar layikan sadarwa ne watau irin su mtn, glo, airtel, da 9mobile kenan. Amma kuma tare da haka akwai wasu ƴan dabaru da mai waya zai yi domin dawo da network ɗinsa ko kuma inganta ƙarfin sa.
A cikin irin dabarun da za'a iya yi akwai kashe waya da kuma kunnawa bayan ƴan mintuna, sau tari hakan yana taimakawa wurin dawo da network, baya ga haka akwai restarting waya wanda kamar shine refreshing kenan, idan akai restarting waya to wayar da kanta zata kashe kanta ta sake kunna kanta watau tayi booting kenan, wannan ma yana taimakawa sosai. Bayan haka kuma ana iya saka ta a flight mode watau air plane mode, duk abu ɗaya ne kuma shima idan anyi akan dace.